Hukumar Lafiya Ta Duniya ta fada aikin jinkai a yankunan da a ke fama da masu tayar da kayar baya a yankin arewa masu gabas na Najeriya

Hukumar Lafiya Ta Duniya ta fada aikin jinkai a yankunan da a ke fama da masu tayar da kayar baya a yankin arewa masu gabas na Najeriya

Kananan hukumomi 15 daga cikin wadanda a ka kwato daga hannun ‘yan tada kayar baya na cikin mawuyacin hali na bukatar kulawa da lafiya

Sanarwar manema labarai

22 ga Agusta 2016 | GENEVA – A

Tawagar jami’an Hukumar lafiya ta Duniya (WHO) na gaggawa ya isa Birnin Maiduguri ranar 19 ga watan Agusta na 2016 domin tantance yanayin bukatun kula da lafiya na jama’a kusan 800,000 da ke yankunan gabashin Najeriya wadanda suka kasance da a hannun ‘yan tayar da kayar baya. Sakamakon haka Hukumar Lafiya ta Duniya ta fada agajin kula da lafiya na gaggawa tare da hadin gwiwar sauran kungiyoyin kasa-da-kasa.  Wannan yunkuri zai taimakawa dubban daruruwan jama’a wadanda suke ciki mawuyacin hali na bukatar aiyukan kula da lafiya.  Fiye da kashi hamsin cikin dari (50%) na asibitocin da ke Jihar Borno ba sa aikin sakamakon rikicin da yankin ya sha fama da shi.

Bayanan da tawagar ta samu ya nuna cewa akwai matsalolin kiwon lafiya tsakanin al’ummomin da ke zaune a kananan hukumomi 15 wadanda da suke a hannun ‘yan tayar da kayar baya.  Kididdigar mace-mace a wasu daga cikin wadannan yankuna ya zarce mizanin bukatar agajin gaggawa har ninki hudu (4).  Har ila yau kuma akwai matsananciyar yunwa da a ke fama da ita a wannan yankin wadda ta kai kimanin kashi 14 daga cikin 100 (14%).  Bugu da kari kuma, a makon jiya ne Najeriya ta sami bullar cutar shan-inna a yara biyu a Jihar Borno, wanda wannan ya faru bayan shekara biyu da kasar tayi ba a sami bullar cutar ba.  Daya daga ciki wannan cuta an same ta ne a karamar hukumar da har yanzu ba a iya shiga da aiyukan kiwon lafiya, sannan dayar kuma an same ta ne a karamar hukumar da kwanannan ne a ke iya shiga domin bayar da aiyuka kula da lafiya.  Akwai kuma yara da yawa da suke fama da cutar kyanda a wadannan yankuna, wanda ya dada rikita halin da yankin ya ke ciki.

Burin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran kungiyoyin kasa-da-kasa, shine na samun raguwar mace-mace da kuma yaduwar cututtuka cikin gaggawa ta hanyar fada aiyukan lafiya domin ceton rai.  Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) za ta yi aiki da jami’an hukumomi na yankunan da kuma kwararru daga sauran hukumomi domin magance barazanar da halin yunwar da yankin ke fama da shi, da kuma, barkewar cututtuka, da kuma tsawon lokaci da yankin yayi babu aiyukan kiwon lafiya.

Aiki a halin da wannan yankin ya ke ciki wani babbab kalu-bale ne kwarai.  Domin akwai karancin albarkatu da kayan aiki da kuma kwararru a yankin.  Halin rashin cikakken tsaro da yankin ke ciki wata babbar matsala ce musamman yadda a ke samun hare-haren ‘yan tayar da kayar baya a kan ma’aikatan agaji a kwanakin nan.  A halin yanzu kuma damina ta yi nisa tare da hasashen afkuwar ambaliyar ruwa a satuttuka masu zuwa.  Shiga wadannan yankuna kuma yana bukatar rakiyar Sojoji ga nisa da kuma rashin kyawun hanya a yankunan.

Amma duk da haka, Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) da sauran kungiyoyi da hukumomi na kasa-da-kasa suna daukar matakan gaggawa domin magance halin da wannan yankin yake ciki.  Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta riga ta aika da kwararru zuwa Najeriya domin aikin gaggawa, da sauran tsare-tsare, da kuma tattata alkaluma domin gabatar da aiyuka yadda ya kamata.  Akwai kuma wani ayarin wannan hukuma ta ajiye a Jihar ta Borno domin taimakawa wajen gabatar da aiyukan rigakafi domin hana yaduwar cutar da bulla.  Gwamnati kuma ta kaddamar da gagarumin shirin shirin rigakafi na gaggawa da gudummawar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran kungiyoyi da hukumomi na kasa-da-kasa.  Kashin farko na zagayen rigakafi ya kusa kammaluwa wanda zai cimma yara miliyan daya. Zagayen shirin rigakfin cutar shan inna masu zuwa  an shirya su daga nan zuwa watan Nuwamba kuma Hukamar Lafiya ta Duniya (WHO) ta aika da magunguna da sauran kayan bukatu haka kuma  sashen ta na ayyukan agaji na gaggawaa za a karfafashi ta hanyar samar da kwararrun ma’aikata acikin yan kwanaki masu zuwa.

Kamar yadda Dr Peter Salama, shugaban Hukumar Lafiya (WHO) ta duniya bagaren kula da shirye shiryen agajin gaggawa ta fuskar kiwon lafiya da kare rikici kamar yadda aka yafaru a arewacin Najeriya  da kasashen da  kewayen kogin Chadi kamar su Chadi da Kamaru da Nijar suna cikin kasashen da ke da hatsarin yada cututtuka ga duniya baki daya gashi kuma sun fi kowace kasa  yawan mace-mace  yara da mata masu juna biyu haka kuma za su iya kasancewa cibiyoyin yada cututtuka da annoba amma mafi yawancin lokuta ba a fiya maida hankali a kan su ba.

Ayyukan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da ya shafi tallafin gaggawa an dasa shi ne a kan dadaddun ayyukan hukumar a Najeriya kamar wajen tallafawa samar da  ingantaccen  shirin kiwon lafiya wanda ya hada da shirin alluran rigakafi, da shirn kula da lafiyar mata da kananan yara da jarirai da kuma da kuma bada ayyuka akan yaki da cuta mai karya garkuwar jiki. A yanzu haka hukumar lafiya ta duniya ta fadada ayyukan gaggawa tare da bada mahimmanci akan ayyukan ceton rayuka musamman yaki da cututtuka da inganta lafiyar kananan yara da mata.Bukatu na kudi domin bangaren kiwon lafiya anyi kiyasin sunkai dala miliyan ashirin da biyar a Najeriya wanda shine zai kula da tsare tsaren ayyukan jinkai wanda a ayanzu haka ake sake nazari tare da kungiyoyin kasa da kasa saboda abubuwan dake faruwa  kwana kwanan nan

________________________________________

Domin samun karin bayani a tuntubi:

Tarik Jašarević
Jami’in sadarwa
Lambar waya: +41 793 676 214
Lambar waya ta Ofis: +41 22 791 5099
Adireshinl shafin yanar gizo: %20%20%20jasarevict [at] who.int ( jasarevict[at]who[dot]int )
Christian Lindmeier
Jami’in sadarwar
Lambar waya: +41 79 500 65 52

Lambar waya ta ofis: +41 22 791 19 48
Adireshin shafin yanar gizo: %20%20%20andemichaelg [at] na.afro.who.int ( andemichaelg[at]na[dot]afro[dot]who[dot]int )